DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeSiyasaNaira dubu 3,000 ba ta isar mutum a Nijeriya - Onoh ya...

Naira dubu 3,000 ba ta isar mutum a Nijeriya – Onoh ya caccaki Omokri

Josef Onoh, shugaban kungiyar tsoffin mambobin majalisar dokokin jihar Enugu, ya caccaki Reno Omokri, wanda aka tsayar da shi a matsayin jakadan Nijeriya mai jiran tantancewa zuwa Mexico, kan ikirarin cewa matsakaicin dan Najeriya zai iya rayuwa cikin sauki da kasafin naira 3,000 a rana.

Da yake magana a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels Television, Omokri ya ce da kansa ya gudanar da bincike a kasuwa domin tabbatar da farashin kayan abinci na yau da kullum.

Ya ce: “Na je kasuwa tare da wani dan jarida, ba tare da jami’an tsaro ba, kuma na tsaya a wurare daban-daban a hanya domin duba farashin kayayyaki. Na duba farashin doya, shinkafa, masara da ’ya’yan itatuwa. A Nijeriya, mutane na iya rayuwa da wannan adadin kudi a rana.

“Amma a Amurka, idan ka yi kokarin rayuwa da wannan adadin kudi a rana, za a dauke ka a matsayin mai fama da talauci. Don haka, dole ne a duba yanayin da ake ciki, domin yanayi yana da matukar muhimmanci.”

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Onoh ya ce bayanin Omokri yana dauke da kura-kurai, kasancewa ya yi nisa da hakikanin yanayin tattalin arzikin Nijeriya, sannan ya nuna rashin kulawa ga halin da al’umma ke ciki.

Ya ce duk da cewa idan aka lissafa naira 3,000 a rana, zai kai kusan naira 90,000 a wata, wanda yake sama da mafi karancin albashin kasa na naira 70,000, wannan lissafi ne kawai da aka ware shi daga sauran abubuwa, wanda ya yi watsi da muhimman abubuwan da suka shafi tsarin tattalin arzikin yan Nijeriya, hauhawar farashin abinci da kuma tashin farashin sauran abubuwan bukata da ba abinci ba.

Onoh ya ce bayanai kan ‘Kudin Abinci Mai Gina Jiki’ da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar sun nuna cewa kudin samar da abinci mai inganci ga mutum daya ya haura naira 1,500 a rana.

Ya ce wannan kudin ya shafi kayan abinci ne kawai, ba tare da hada muhimman kudaden da ake kashewa wajen girki da rayuwa ba, kamar gas din girki, kananzir, gawayi da ruwan sha. Ya kara da cewa a manyan birane, farashin kayan abinci na yau da kullum ya wuce hasashen da aka yi a baya.

“A halin yanzu, kwando daya na barkono sabo yana kusa da naira 9,000, yayin da tumatir sabo ke kusan naira 12,000. Farashin hatsi, wake da tubers kamar shinkafa da wake na ci gaba da hauhawa a kowace shekara saboda matsalolin sufuri da rarraba kayayyaki.

Onoh ya ce ikirarin Omokri ya kara zama abin tambaya idan aka yi la’akari da bambancin yanayin tattalin arziki tsakanin yankuna.

Onoh ya ce amfani da mafi karancin albashin naira 70,000 wajen tabbatar da cewa naira 3,000 a rana ta isa mutum ya rayu, hujja ce da ke nuna koma baya a fannin tattalin arziki.

Ya ce irin wannan tunani yana kokarin mayar da matsanancin talauci tamkar abu na yau da kullum, maimakon magance matsalolin tattalin arziki da suka jefa ’yan Nijeriya cikin mawuyacin hali.

Onoh ya bukaci Omokri da ya daidaita bayanansa da ainihin matsin tattalin arzikin da talakawan Nijeriya ke fuskanta, maimakon gabatar musu da alkaluman tattalin arziki na siyasa domin cimma wata manufa ta siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata