Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bukaci tsohon ɗan wasan Nijeriya, Joseph Yobo, da ya isar wa ‘yan wasan saƙon cewa ‘yan Nijeriya ba su ji daɗin rashin samun gurbin shiga Kofin Duniya na 2026 ba.
Wike ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wani taro da Yobo ya halarta, inda ya ce rashin samun tikitin gasar ya ɓata wa miliyoyin ‘yan Nijeriya rai saboda irin ƙaunar da suke yi wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar.
