DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeKetareAn ware lokutan shiga Hijr Isma’ila da ke jikin Dakin Ka‘aba

An ware lokutan shiga Hijr Isma’ila da ke jikin Dakin Ka‘aba

Hukumar kula da harkokin Masallacin Harami da Masallacin Annabi da ke Saudiyya ta sanar da sabbin lokutan shiga Hijr Isma’ila (Hateem), wuri mai albarka da ke kusa da Ka’aba, ga maza da mata.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, mata za su iya shiga Hijr Isma’ila kowace rana daga karfe 6:00 na safe zuwa 9:00 na safe, yayin da aka ware wa maza damar shiga daga karfe 10:00 na dare zuwa 1:00 na dare.

Hukumar ta ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tsara kai-da-kawowar masu ibada da kuma samar da yanayi mai sauki da aminci ga masu ziyartar Masallacin Harami.

Hijr Isma’ila, wanda ake kira Hateem, na daga cikin wuraren da Musulmi da dama ke kwadayin yin sallah da addu’a a cikinsa saboda falalarsa da kusancinsa da dakin Ka’aba mai tsarki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata