DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeNishadi'Kabilar da mata ke sha’awar maza masu ƙaton ciki'

‘Kabilar da mata ke sha’awar maza masu ƙaton ciki’

Allah ɗaya gari bambam!

A yayin da a kasashe da dama ake kallon siririn jiki a matsayin alamar kyau, wata kabila a kasar Habasha mai suna Bodi na da wata al’ada ta daban inda ake ganin maza masu manyan ciki sun fi jan hankalin mata kuma suna da matsayi a al’umma.

Kamar yadda jaridar Times of India ta ruwaito, ƙabilar na gudanar da wata gasa mai suna Ka’el a kowace shekara, inda samari ke fafatawa domin zama mutumin da ya fi kowa kiba da ƙaton ciki.

A al’adar ƙabilar, ana kallon babban ciki a matsayin alamar ƙarfi da daraja, kuma wanda ya lashe gasar kan zama gwarzon ƙabilar har tsawon rayuwarsa.

Rahotanni sun nuna cewa kowane iyali a ƙabilar kan zaɓi wani saurayi mara aure ya wakilce ta a gasar.

Da zarar an zaɓe shi, sai ya killace kansa a cikin bukka na tsawon watanni shida ba tare da yin wani aiki mai wahala ko fita yawon gari ba.

A wannan lokaci, ana shayar da shi madarar shanu da kuma jinin shanu domin ya ƙara kiba cikin sauri.

An bayyana cewa ba sa kashe shanun saboda ƙabilar na kallon su a matsayin dabbobi masu tsarki. Maimakon haka, ana huda jijiyar dabbar domin a debo jini sannan daga baya a rufe wurin da laka.

Ana hana su motsa jiki

A lokacin gasar, samarin ba sa yin wani aiki ko motsa jiki domin kada su rage kiba.

Haka kuma ana hana su hulɗa da mata yayin shirin gasar, yayin da sauran mutanen ƙabilar ke kula da su sosai saboda muhimmancin gasar a al’adarsu.

Ranar fitowa bainar jama’a

Bayan watanni shida, samarin kan fito bainar jama’a jikinsu shafe da toka da laka, suna nuna girman tumbinsu yayin da jama’a ke kallon wanda zai zama zakaran shekara.

Wasu ma kan sanya kayan ado da gashin jimina a kansu a matsayin wata tsohuwar al’ada ta ƙabilar.

Wanda ya fi kowa kiba shi ne ake ayyana a matsayin gwarzo, kuma ko da babu kyautar kuɗi, mutumin kan samu girma da mutunci sosai a cikin al’umma.

Rahotanni sun ce mata da dama a ƙabilar kan fi sha’awar maza masu manyan jiki saboda ana kallon su a matsayin masu ƙarfi da daraja.

Wani mai daukar hoto ya bayyana abin da ya gani

Wani mai daukar hoto mai suna Eric Lafforgue, wanda ya samu damar ganin yadda ake gudanar da bikin, ya ce samarin kan fara ranarsu ne da shan jini da madara.

Ya ce shan irin wannan ruwa mai yawa kan jawo musu rashin jin daɗi, amma duk da haka suna dagewa saboda son lashe kambun.

Al’adar na fuskantar barazana

Rahotanni sun nuna cewa ƙabilar Bodi na da matukar sirri kan al’adunta, inda ba kasafai suke bari baki su shiga ƙauyukansu ko kallon bukukuwansu ba.

Sai dai kamar sauran tsofaffin al’adu, wannan ma na fuskantar barazanar bacewa sakamakon sauye-sauyen zamani.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata