Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce son zuciya da rashin kula da muhalli daga hannun bil’adama ne suka haddasa dumamar yanayi da matsalolin sauyin yanayi a duniya.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a wani taro da aka shirya a Kano domin karrama tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Nijeriya NBA, Abubakar Mahmoud, da gidauniyarsa ta kula da muhalli da dorewar rayuwa.
Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, tsohon shugaban ya ce ayyukan mutane sun lalata daidaiton da Allah ya halicci duniya a kai. Obasanjo ya bayyana cewa sauyin yanayi na kara tsananta ne saboda yadda mutane ke amfani da albarkatun kasa ba tare da kula da muhalli ba.
A cewar tsohon shugaban kasar, “Allah ya halicci duniya cikin daidaito, amma mu mutane saboda son kai da sakaci mun yi barna fiye da alheri ga muhalli.”
Ya kuma bayyana cewa ya dasa bishiyoyi sama da miliyan 3.5 a matsayin gudunmawarsa wajen rage matsalar sauyin yanayi da kare muhalli.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar Kano, Dahiru Hashim, ya yabawa wannan shiri tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta tallafa wajen dorewar aikin.
Ya ce gwamnatin Kano ta amince da bayar da tsirrai guda 10,000 domin tallafawa gidauniyar Mahmoud Environmental and Sustainable Trust.
Shi ma Abubakar Mahmoud ya ce manufar shirin ita ce kare muhalli da kuma tabbatar da an adana albarkatun kasa domin amfanin al’ummomi na yanzu da masu zuwa.
Ya ce aikin da ya fara tun farko yanzu ya bunkasa zuwa wani babban shiri da ke taimakawa wajen kare kauyuka da nau’o’in tsirrai daban-daban.
Taron ya samu halartar manyan baki da suka hada da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso, da tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, tare da jami’an gwamnatin Kano da sauran masu ruwa da tsaki.
