Majalisar Wakilan Nijeriya ta bayyana cewa tun bayan ƙaddamar da Majalisa ta 10 a watan Yunin 2023, an gabatar da jimillar ƙudirin dokoki 2,747, inda aka amince da 363 daga cikinsu.
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Majalisar, Akin Rotimi, tare da Shugaban Kwamitin Dokoki da Harkokin Majalisa, Francis Waive, sun ce mafi yawan ƙudirorin dokokin sun fito ne daga ‘yan majalisa masu zaman kansu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi ya ce sun kuma bayyana cewa har yanzu ƙudiri 1,782 na jiran karatu na biyu, 323 na hannun kwamitocin dindindin, yayin da aka haɗa ƙudiri 89 wuri guda, aka kuma yi watsi da guda biyar.
A cewarsa, Majalisar ta kuma ci gaba da gudanar da ayyukan sa ido ta hanyar karɓar ƙorafe-ƙorafen jama’a da gabatar da muhimman kudurori domin magance matsalolin da ƙasa ke fuskanta.
Rahoton ya fito ne yayin bikin cika shekaru uku na Majalisa ta 10, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas.
Majalisar ta ce tana ci gaba da mai da hankali kan gyaran kundin tsarin mulki, gyaran zaɓe, tsaro, bunƙasa tattalin arziki da inganta ayyukan gwamnati a Nijeriya.
