Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ƙara matsa wa Shugaba Bola Tinubu lamba kan matsalar tsaro, inda ya yi zargin cewa har sama da kwanaki 50 bayan sace ɗalibai da malamai 37 a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, shugaban bai taɓa kiran Gwamnan Seyi Makinde ba kan lamarin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Obi ya ce ya samu wannan bayani ne yayin wata ziyara da ya kai wa Makinde a Ibadan tare da Pat Utomi, inda suka tattauna kan matsalar tsaron jihar tare.
Ya ce rashin wannan tausayi alama ce ta gazawar jagoranci da rashin ja a jiki, yana mai kwatanta lamarin da yadda tsoffin shugabannin ƙasa ke hulɗa da gwamnonin jihohi idan aka samu manyan hare-hare a jihohin kasar.
Obi ya kuma sake kira ga Tinubu da ya sauka daga mulki ko kuma ya ƙi tsayawa takara a zaɓen 2027, yana cewa wannan kira na kishin ƙasa ne ba na siyasa ba.
Kodayake a nata ɓangaren, Fadar Shugaban Ƙasa ta ci gaba da cewa jami’an tsaro na matsa kaimi wajen yaƙi da masu aikata laifuka tare da neman haɗin kan ‘yan Najeriya wajen shawo kan lamarin.
