Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce Shugaba Bola Tinubu tare da hukumomin tsaro na ƙara ƙaimi wajen magance matsalolin rashin tsaro da suka haɗa da ta’addanci da garkuwa da mutane a faɗin Nijeriya.
Jaridar Punch ta ruwaito ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ta karɓi jakadan ƙasar Qatar a Nijeriya, Yousef Bin Hassan Al-Hail, da kuma jami’in ofishin jakadancin, Khalifa Al-Khalifa, a wata ziyarar girmamawa da suka kai ofishinta.
Oluremi Tinubu ta ce Nijeriya ƙasa ce mai faɗi, mai cike da al’adu da kuma mutane masu zaman lafiya, inda ta jaddada cewa gwamnati na ci gaba da aiki tuƙuru domin dawo da cikakken tsaro.
Ta kuma ƙarfafa matasa su rika zagaya sassan ƙasar domin sanin arzikinta, tana mai cewa fannin yawon buɗe ido na ɗaya daga cikin manyan damar samar da ayyukan yi, baya ga albarkatun mai, iskar gas da ma’adinan lithium.
A nasa jawabin, Jakadan Qatar, Yousef Bin Hassan Al-Hail, ya ce tsoron da yake yi game da zuwa Nijeriya sakamakon bayanan da ya gani a kafafen sada zumunta ya kau gaba ɗaya bayan isowarsa ƙasar.
Ya yabawa Nijeriya kan yanayinta, mutanenta da kyawawan wuraren yawon buɗe ido, tare da kira da a ƙara ƙarfafa alaƙar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Qatar, musamman a fannonin sufurin jiragen sama da yawon buɗe ido.
Jakadan ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya su guji yaɗa ƙarya da cin zarafi a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na bata sunan ƙasar a idon duniya.
