Wata mata mai shekara 27 daga ƙasar Canada mai suna Carolina Moreno ta ba da labarin yadda ta haifi ɗanta na uku ba tare da ta sani ba, bayan ta yi barci yayin nakuda a asibiti.
Jaridar Punch ta ruwaito ta ce an saka mata maganin tayar da nakuda da kuma allurar rage radadi, lamarin da ya sa ta yi barci mai nauyi.
A cewarta, yayin da ma’aikatan jinya ke neman bugun zuciyar jaririn ta na’urar sa ido, ba su fahimci cewa jaririn ya riga ya fito da kansa ba.
Da aka buɗe bargon da ke kanta, sai aka tarar da jaririn kwance a ƙarƙashinta ba tare da yana kuka ba, abin da ya tayar da hankalin kowa da ke ɗakin karɓar haihuwar.
Mahaifiyar jaririn ta ɗauke shi nan take ta motsa shi har ya fara kuka. Daga baya likitoci suka tabbatar da cewa jaririn yana cikin ƙoshin lafiya.
Yanzu haka dai yaron yana da wata uku a duniya, kuma mahaifiyarsa ta ce yana girma cikin koshin lafiya kuma shi ne mafi natsuwa a cikin ‘ya’yanta uku.
