DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaSheik Jingir ya bukaci Tinubu ya yi adalci ga Musulmi da Kiristocin...

Sheik Jingir ya bukaci Tinubu ya yi adalci ga Musulmi da Kiristocin Nijeriya

Shugaban Ƙungiyar JIBWIS mai hedkwatar Jos a Nijeriya, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bukaci shugaban Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da adalci da gaskiya ga dukkan ’yan Nijeriya, ba tare da la’akari da addini ko jam’iyyar siyasa ba.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Jingir ya bayyana hakan ne a wani taron ƙasa mai taken “inganta harkokin siyasa da adalci a matsayin hanyar samar da haɗin kai da ci gaba a Nijeriya”, wanda aka gudanar a cibiyar taro ta Sadeeqa da ke Jos, jihar Plateau.

Malamin ya ce goyon bayansa ga tikitin shugaban ƙasa da mataimakinsa musulmi ba ya nufin yana ƙin kiristoci ko sauran waɗanda ba musulmi ba. Ya ce matsayinsa na siyasa bai samo asali daga ƙiyayya ga wani addini ba.

Jingir ya kuma yi kira ga Tinubu da kada ya nuna wariya ga waɗanda ba musulmi ba ko kuma ’yan Nijeriya da ba sa cikin jam’iyyarsa. Ya jaddada cewa shugaban ƙasa ya kamata ya tafiyar da mulki bisa adalci da gaskiya ga kowa.

Sheikh Jingir ya bayyana cewa kowane ɗan Nijeriya na da ’yancin zaɓar ɗan takarar da yake ganin ya dace da shi a lokacin zaɓe, ba tare da an tilasta masa yin la’akari da addinin ɗan takarar ba.

Ya kuma bayyana cewa a baya ya taɓa zaɓar wani ɗan takarar gwamna kirista a jihar Plateau, inda ya ce abin da ya fi la’akari da shi shi ne wanda zai tabbatar da adalci da wakilcin musulmi da sauran al’umma a cikin gwamnati.

Dangane da zaɓen gwamnan Plateau na shekarar 2007, jingir ya ce ya ƙi goyon bayan wani ɗan takarar kirista bayan ya lura cewa babu wani musulmi a cikin tawagar da ta raka shi wajen neman goyon bayansa. Ya ce wannan ya nuna cewa abin da ya kamata ya zama tushen zaɓin siyasa shi ne adalci, wakilci da kare muradun al’umma, ba ƙiyayya ta addini ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata