Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a wasu sassan jihar Katsina, dubban mazauna yankunan karkara na ci gaba da tserewa daga gidajensu sakamakon ci gaba da kai hare-hare, kisa, garkuwa da mutane, da kuma satar shanu.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa al’ummomin da lamarin ya shafa sun hada da kananan hukumomin Malumfashi, Musawa, Matazu, Dutsinma, Bakori, Faskari, Kankara, da Dandume. A cewar mazauna yankunan, yarjejeniyar da aka kulla a garin Kakumi da ke karamar hukumar Bakori ta gaza samar da isasshen tsaron da zai ba su damar komawa garuruwansu da gonakinsu cikin kwanciyar hankali.
Wani manomi da ya rasa muhallinsa mai suna Audi Yaro, ya bayyana yadda rikicin ya mayar da masu hannu da shuni mabarata, inda ya ce, “Da yawa daga cikinmu ba matalauta ba ne kafin wannan matsala ta taso; muna da gonaki da dabbobi kuma muna ciyar da iyalanmu tare da biyan kudin makaranta, amma bayan mun gudu mun rasa komai namu.”
A halin da ake ciki, mazauna yankunan sun koka da cewa yarjejeniyar zaman lafiyar ta zama tamkar tarko a gare su, domin idan suka kare kansu ana zarginsu da karya dokar zaman lafiya, idan kuma ba su yi komai ba ‘yan bindigar na ci gaba da farmakarsu.
Baya ga asarar dukiyoyi, lamarin ya jefa mata da kananan yara cikin hadarin cin zarafi ta hanyar lalata a birane. Haka kuma wani mai gidan abinci a birnin Katsina, Malam Salisu Daga, ya bayyana cewa tsananin yunwa ya sa wasu iyaye sayar da maganin tamowa na yara (RUTF) da ake ba su domin su sami kudin abincin sauran iyali, yayin da wasu ke karbar aron yara marasa lafiya domin karbar tallafin.
Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Katsina kan sha’anin ‘yan Bindiga, Sa’idu Ibrahim Danja, ya bayyana cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar ya kai 30,000.
Ya kara da cewa gwamnati ta ba da umarnin cewa duk yaron da rikicin ya raba da muhallinsa zai iya shiga kowace makaranta ba tare da an nemi takardun da ya bari a gida ba, tare da bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara aikin sake gina makarantu, asibitoci da hanyoyi domin share fagen komawar jama’a garuruwansu.
