Amfani da motocin ɗaukar marasa lafiya (ambulan) wajen ɗaukar gawarwaki domin binne su na iya ƙara haɗarin yaɗuwar cututtuka tare da janyo ɓarkewar annoba, musamman idan mamacin ya mutu sakamakon cuta mai yaɗuwa.
Jaridar Punch ta bayyana cewa ƙwararrun likitocin kiwon lafiyar al’umma ne suka gargaɗi jama’a kan hakan, inda suka bayyana cewa gawa na iya fitar da ruwan jiki mai ɗauke da ƙwayoyin cuta, wanda hakan ke mayar da harkokin ɗauka da jigilar gawa wata babbar barazana ga lafiyar al’umma.
Masanan sun bayyana cewa amfani da motar asibiti guda ɗaya wajen ɗaukar mai rai da kuma matacce ba tare da an wanke ta da maganin kashe ƙwayoyin cuta ba, na jefa ma’aikatan lafiya, direbobi, sauran marasa lafiya da fasinjoji cikin haɗarin kamuwa da miyagun cututtuka.
Wannan gargaɗi na zuwa ne kwanan nan bayan da gwamnatin jihar Akwa Ibom ta haramta amfani da motocin asibiti wajen ɗaukar gawa a faɗin jihar, inda kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Ekem John, ya bayyana cewa duk motar asibiti da aka kama tana ɗaukar gawa za a ƙwace ta, yana mai jaddada cewa ya kamata a yi amfani da motoci na musamman da aka ware domin gawa (hearse).
Da yake magana da jaridar ta Punch, wani farfesa a fannin kiwon lafiyar al’umma da nazarin yaɗuwar cututtuka a asibitin koyarwa na Jami’ar Legas (LUTH), Adebayo Onajole, ya bayyana cewa idan ba a wanke motar ba sosai, cututtuka masu kisa kamar Ebola za su iya shafar marasa lafiya da aka ɗauka a cikinta daga baya.
Ya buƙaci masu gudanar da motocin da su ware motoci daban domin ɗaukar marasa lafiya masu rai, da kuma na musamman domin ɗaukar gawarwaki.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar masu ba da kulawar kiwon lafiya a Nijeriya, Dakta Austine Aipoh, ya bayyana cewa idan mutum ya mutu sakamakon cuta mai yaɗuwa kamar kwalara ko Ebola, ruwan jikinsa na iya ɓata motar, wanda idan aka ɗauki wani mara lafiya zai iya kamuwa da wata cutar ta daban kafin ya isa asibiti.
Ya buƙaci a riƙa tsaftace dukkan motocin ɗaukar marasa lafiya yadda ya kamata a kowane lokaci.
