Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya bayyana cewa za a sanar da ƙarin naɗe-naɗe yayin da kwamitin ke ci gaba da faɗaɗa tsarinsa a faɗin ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa darektan sadarwa na kwamitin, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce jerin sunayen da aka fitar kwanan nan mataki ne mai muhimmanci a tsarin tafiyar, amma ba shi ne na ƙarshe ba.
Shaibu ya ce, “Tafiyar yaƙin neman zaɓen na ci gaba da bunƙasa. Ana ci gaba da tattaunawa, kuma za a raba ƙarin ayyuka yayin da tsarin ke faɗaɗa a faɗin ƙasa. Atiku Abubakar na sane da irin sadaukarwar da waɗanda suka tsaya tare da shi a tsawon shekaru suka yi. Ana tuna biyayya, ana girmama sadaukarwa, kuma ana daraja abota.”
Ya buƙaci waɗanda ba su ga sunayensu a jerin farko ba da su yi haƙuri, yana mai jaddada cewa babu wanda zai ɗauka an manta da shekarun da ya kwashe yana sadaukarwa.
A cewar Shaibu, a kwanaki masu zuwa kwamitin zai sanar da shugabanninsa na shiyyoyi da jihohi, ƙarin manyan naɗe-naɗe, da kuma sauran ɓangarorin da za su kai har zuwa matakin gundumomi da rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar.
Haka kuma, ya bayyana cewa kwamitin na ƙarfafa tawagarsa ta tsare-tsare domin haɗa ƙwararrun ‘yan Nijeriya masu gogewa da hangen nesa a fannonin da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa a ƙasar, ciki har da tsadar rayuwa, wadatar abinci da noma, tsaro, wutar lantarki, samar da ayyukan yi, masana’antu, ilimi, kiwon lafiya, da fasahar zamani.
