Wani jigo a jam’iyyar ADC, Salihu Tanko Yakasai, ya zargi gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf da hana jam’iyyun hamayya kafa allunan yaƙin neman zaɓe a faɗin jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Yakasai ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi zargin cewa gwamnatin jihar na tauye musu damar tallata manufofinsu na siyasa.
Yakasai ya ce, “Ban taɓa tunanin cewa irin danniyar da ake zargin APC da yi a wasu jihohin za ta iya faruwa a Kano ba.” Ya ƙara da cewa ana hana ADC damar amfani da allunan tallace-tallace domin isar da saƙonninta ga al’ummar jihar, inda ya buƙaci Gwamna Yusuf da ya yi duba ga yadda mulki yake mai ƙarewa.
Hakazalika, Adnan Mukhtar Tudun Wada, mai taimaka wa ɗan takarar gwamna na ADC, Ibrahim Ali Little, ya bayyana cewa gwamnati ta ba da umarnin cire allunan jam’iyyar ADC a faɗin jihar.
Tudun Wada ya bayyana matakin a matsayin cin zarafin dimokuraɗiyya tare da ƙuntata wa ƴan siyasa a Kano, yana mai cewa ko a lokacin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, an bai wa ‘yan adawa damar kafa alluna bisa ƙa’idar doka.
Shi ma ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a ƙarƙashin ADC, Mussadiq Tofa, ya bayyana cewa wani kamfanin talla ya mayar masa da kuɗinsa tare da cire allunansa bayan samun umarni daga hukumar kula da allunan talla ta Jihar Kano (KASA). Ya yi iƙirarin cewa kamfanin ya shaida masa allunan ba su dace da muradun gwamnati mai ci ba, kuma idan suka ƙi bi za a iya soke musu lasisin aiki.
Sai dai da aka tuntuɓe shi, Darakta Janar na hukumar KASA, Kwamared Kabiru Dakata, ya musanta waɗannan zarge-zarge. Ya bayyana cewa hukumar ba ta hana wata jam’iyyar siyasa damar kafa allunan talla ba, matuƙar ta bi ƙa’ida ta nemi izini tare da biyan kuɗin da suka dace.
Dakata ya ce, “Ba ma nuna bambanci ga kowace jam’iyyar siyasa. Abin da ake buƙata wajen kafa allunan yaƙin neman zaɓe shi ne abin da ake buƙata ga dukkan tallace-tallacen waje. Ka biya kuɗin da suka dace kuma ka sami izinin kafawa. Za mu cire duk wani allon da aka kafa ba tare da izini ba, shi ke nan.”
