DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 3, 2026
HomeSiyasaZan janye daga takarar mataimakin Atiku, na goyi bayan Tinubu idan fetur...

Zan janye daga takarar mataimakin Atiku, na goyi bayan Tinubu idan fetur ya koma N600 – Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma mataimakin ɗan takarar jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya ce zai janye daga takarar mataimakin Atiku Abubakar tare da yi wa Shugaba Bola Tinubu kamfen, idan farashin man fetur ya koma Naira 600 kan lita daga gobe.

Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya ce zai je gidan mai da kansa domin tabbatar da farashin idan ya sauka zuwa N600.

Ya ce cire tallafin man fetur ba tare da samar da isassun matakan rage wa ’yan Nijeriya radadin tsadar rayuwa ba, ya ƙara wa jama’a wahala.

Amaechi ya kuma bayyana zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a matsayin wani muhimmin zaɓi ga ’yan Nijeriya, inda ya yi zargin cewa Tinubu na gasa wa talaka aya a hannu.

Bugu da ƙari, tsohon ministan sufurin ya zargi gwamnatin Tinubu da cin hanci da rashawa fiye da gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, yana mai cewa bambancin shi ne yadda ake ganin cin hancin a ƙarƙashin gwamnatin yanzu a fili.

Sai dai Amaechi ya musanta cewa ya taɓa shiga harkar cin hanci a lokacin da yake ministan sufuri a gwamnatin Buhari, yana mai cewa ya shirya fuskantar duk wanda zai tabbatar da zargin cewa shi maƙaryaci ne ko mai cin hanci.

Haka kuma, ya soki gwamnatin Tinubu kan ayyukan more rayuwa, inda ya ƙalubalanci gwamnati ta ambaci wani babban aikin da ta kammala tun bayan hawanta mulki, tare da kwatanta hakan da kammala aikin layin dogo Abuja zuwa Kaduna a farkon mulkin Buhari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata