DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, October 1, 2026
HomeSiyasaJam’iyyun adawa na neman haɗin kai kan takarar shugaban ƙasa a 2027...

Jam’iyyun adawa na neman haɗin kai kan takarar shugaban ƙasa a 2027 – Bincike

Jam’iyyun adawa a Nijeriya na ƙara tattaunawa kan yiwuwar tsayar da ɗan takara guda a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa shugabannin wasu jam’iyyun adawa sun gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, a Abuja ranar Talata da dare.

Wannan yunƙurin dai na da nufin samar da ɗan takara guda da zai fafata da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen mai zuwa.

Taron na daga cikin ƙoƙarin G-100, wata ƙungiyar ’yan siyasa da ke neman haɗa jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.

Rahoton ya ce jam’iyyun da ake tattaunawa a kansu sun haɗa da ADC, PDP, NDC, PRP, SDP da APM.

Manufar yunƙurin ita ce samar da matsaya ɗaya tsakanin jam’iyyun adawar gabanin zaɓen 2027.

Sai dai har yanzu ba a fayyace ko ’yan takara da magoya bayansu za su amince da janyewa domin goyon bayan ɗan takara guda ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata