DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, October 11, 2026
HomeSiyasaDan’iya ya bukaci Gwamnan Sokoto ya bayyana kuɗaɗen da ya samu da...

Dan’iya ya bukaci Gwamnan Sokoto ya bayyana kuɗaɗen da ya samu da yadda aka kashe su

Ɗan takarar gwamnan Jihar Sokoto na jam’iyyar ADC, Manir Dan’iya, ya buƙaci Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana adadin kuɗaɗen da gwamnatinsa ta samu da kuma yadda ta kashe su daga watan Mayun 2023 zuwa Satumbar 2026.

Dan’iya ya ce bayyana bayanan kuɗaɗen zai taimaka wa al’ummar jihar wajen tantance ayyukan gwamnan gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Abdullahi, ya fitar ranar Lahadi, a matsayin martani ga kalaman Gwamna Aliyu na cewa APC za ta yi amfani da ayyukan da ta gudanar wajen neman sake zaɓensa.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Gwamna Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Gidan Gwamnati da ke Sokoto, bayan ya idar da sallar Juma’a, inda ya ƙalubalanci jam’iyyun adawa su gabatar da ayyukan da suka yi maimakon kai wa juna hare-hare na siyasa.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta yi kamfen ne bisa ayyukan da ta gudanar domin amfanin jama’a, yana mai cewa ayyukanta za su bayyana irin nasarorin da ta samu a lokacin zaɓe.

Sai dai Dan’iya ya ce duk da goyon bayansa ga kamfen da ya ta’allaka kan ayyuka, dole ne gwamnati ta bayyana kuɗaɗen da ta samu da yadda ta kashe su domin jama’a su iya tantance ayyukanta.

Ya buƙaci Gwamna Aliyu ya bayyana adadin kuɗaɗen da jihar ta samu daga Asusun Tarayya, kuɗaɗen shiga da ta samar da kanta, da kuma jimillar kuɗaɗen da ta kashe a cikin lokacin da ya ambata.

Dan’iya ya kuma nemi a fitar da cikakken bayani kan kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi 23 na jihar, ciki har da rabonsu na kowane wata daga Asusun Tarayya, kuɗaɗen shiga da suka samar, cire-ciren da aka yi da kuma yadda suka kashe kuɗaɗen wajen ayyukan jama’a.

Ya ce wallafa bayanan kuɗaɗen tare da farashin ayyuka, sunayen ’yan kwangila, lokacin kammala ayyukan da kuma hujjojin kammalawarsu zai bai wa jama’a damar tantance abin da gwamnati ta aiwatar bisa bayanan da za a iya tabbatarwa.

Ɗan takarar ADC ɗin ya kuma nuna damuwa kan ko kashe kuɗaɗen da gwamnati ta yi ya haifar da sauyi a rayuwar jama’a, musamman a fannonin tsaro, ilimi, lafiya, samar da ruwa, jin daɗin ma’aikata, rashin aikin yi da kayayyakin more rayuwa.

Ya buƙaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan ayyukan da ake da tambayoyi game da kuɗaɗensu, matsayin kammalawarsu ko amfaninsu ga jama’a, yana mai cewa ya kamata a binciki zarge-zargen ƙarin farashin ayyuka, ayyukan da ba a kammala ba da kuma kashe kuɗi ba tare da sakamakon da ya dace ba.

Dan’iya ya ce bai kamata a auna nasarar gwamnati kawai da sanar da ayyuka, bayar da kwangiloli ko fitar da jimillar kuɗaɗen da aka kashe ba, sai dai a kwatanta kuɗaɗen da aka samu da waɗanda aka kashe, ayyukan da aka kammala da kuma ingancin hidimomin da jama’a ke samu.

Ya ƙara da cewa ya kamata a yi amfani da ma’aunin riƙon amana iri ɗaya wajen tantance gwamnatin jiha da dukkan ƙananan hukumominta 23, domin kuɗaɗen gwamnati na al’umma ne.

A ƙarshe, ɗan takarar ya buƙaci Gwamna Aliyu ya wallafa cikakken rahoton kuɗaɗen shiga da kashe kuɗaɗe daga Mayun 2023 zuwa Satumbar 2026, wanda zai ƙunshi kuɗaɗen da aka samu daga Asusun Tarayya, kuɗaɗen shiga na cikin gida, sauran hanyoyin samun kuɗi, cire-cire da kuma kuɗaɗen gudanarwa da ayyukan raya ƙasa.

Ya ce muhawarar siyasa gabanin zaɓen 2027 ya kamata ta ta’allaka kan bayanan da jama’a, ’yan jarida, masu binciken kuɗi da hukumomin da abin ya shafa za su iya tantancewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata