Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Kaduna ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar domin ƙalubalantar matakin babbar kotun jihar Kaduna na ƙin amincewa da sabuwar buƙatarsa ta beli.
A cewar takardar hukuncin kotun, alƙalai uku na kotun ɗaukaka ƙarar sun yanke hukuncin ne baki ɗaya a ranar Alhamis, inda suka bayyana cewa El-Rufai ya gaza gabatar da sabbin hujjoji ko wasu yanayi na musamman da za su sa kotun ta soke matakin ƙaramar kotun na hana shi beli.
Hukuncin da mai shari’a Onyekachi Aja Otisi ya jagoranta ya tabbatar da matakin babbar kotun jihar Kaduna, wadda ta ƙi amincewa da buƙatar belin El-Rufai karo na biyu a ranar 10 ga yuni, 2026, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito
El-Rufai, wanda ya shugabanci Jihar Kaduna daga shekarar 2015 zuwa 2023, na fuskantar shari’a a gaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka (ICPC), bisa zargin aikata almundahanar kuɗi a lokacin mulkinsa.
Tsohon gwamnan ya musanta aikata laifin, tare da ƙalubalantar dalilan da suka sa aka ci gaba da tsare shi.
Tun da farko, Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi watsi da buƙatar belin da tsohon gwamnan ya shigar, tare da bayar da umarnin gaggauta sauraron shari’ar.
Bayan rashin gamsuwa da wannan hukunci, El-Rufai ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara.
Kotun Daukaka Karar ta bayyana cewa ƙaramar kotun ta yi amfani da ikon shari’a da doka ta ba ta yadda ya kamata wajen ƙin amincewa da belin, tana mai cewa hukuncin ya dogara ne da shaidun rantsuwa da ɓangarorin biyu suka gabatar.
Mai Shari’a Otisi ya ce: “Babu shakka, bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki, ana ɗaukar wanda ake ƙara a matsayin marar laifi har sai an tabbatar da laifinsa.”
Ya ƙara da cewa tantance shaidun rantsuwa da kotun shari’ar farko ta yi dangane da yiwuwar katsalandan a shari’a ba yana nufin ta ayyana El-Rufai a matsayin mai laifi ba ne.
Kotun ta kuma yi la’akari da hujjar El-Rufai cewa komawarsa da kansa hannun jami’an tsaro bayan halartar jana’izar mahaifiyarsa da ta rasu na nuna cewa ba zai gudu daga shari’a ba.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sakin da aka yi masa domin halartar jana’izar, da kuma komawarsa hannun jami’an tsaro daga baya, sun kasance hujjoji masu ƙarfi da ya kamata a yi la’akari da su wajen ba shi beli.
