DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, October 11, 2026
HomeSiyasaMakinde ya bukaci Tinubu ya bayyana tsarin kayyade farashin fetur

Makinde ya bukaci Tinubu ya bayyana tsarin kayyade farashin fetur

Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban Lada na jam’iyyar Alliance People’s Movement (APM), Seyi Makinde, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana tsarin da ake bi wajen ƙayyade farashin man fetur domin ’yan Nijeriya su fahimci yadda ake lissafa kuɗin da suke biya a gidajen mai.

Makinde ya yi wannan kira ne a ranar Asabar a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, yayin taron tattaunawar jam’iyyar APM da masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso Gabas, gabanin zaɓen shekarar 2027.

Premium Times ta ruwaito ya ce bayyana tsarin farashin zai bai wa ’yan Nijeriya damar fahimtar yadda ake kayyade farashin fetur da kuma ba da gudummawarsu kan yadda za a inganta tsarin.

Gwamnan ya ce, ya kamata gwamnati ta kasance ta kowa da kowa, ba wai mutanen da ke kusa da masu mulki kawai ba.

Kiran na Makinde na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan hauhawar farashin fetur da kuma matakan da Gwamnatin Nijeriya ke ɗauka domin rage wa ’yan ƙasa nauyin tsadar rayuwa.

A ranar Juma’a, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya sanar da tsawaita rangwamen farashin fetur da ya fara a ranar 1 ga Oktoba zuwa 31 ga Oktoba a gidajen mansa da ke faɗin ƙasar.

Kamfanin ya ce an ƙaddamar da rangwamen ne domin ɗan rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin tsadar man fetur a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ke fuskantar ƙarin tsada sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai NNPC ya bayyana cewa rangwamen bai nuna an dawo da tallafin man fetur ba, kuma ba ya nufin za a samu farashi iri ɗaya a duk gidajen mai na ƙasar. Kamfanin ya ce tsarin farashin kasuwa ne ke ci gaba da aiki.

A yayin taron, Makinde ya kuma soki manufofin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa ba su kawo gagarumin sauyi a halin da ƙasar ke ciki ba. Ya yi tambayoyi kan shirye-shiryen amfani da iskar gas ta CNG, motocin lantarki, tsarin sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida da kuma matakan yaƙi da rashin tsaro da talauci.

Makinde ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, zai tunkari matsalolin ƙasar da gaskiya tare da shigar da ’yan Nijeriya cikin samar da mafita.

Ya kuma yi alƙawarin kafa gwamnatin wucin gadi ta haɗin kan ƙasa wadda za ta bai wa mutane daga shiyyoyin shida damar bayar da gudummawa wajen tafiyar da harkokin ƙasa, maimakon wani yanki ya mamaye tsarin mulki.

A nasa jawabin, jagoran jam’iyyar APM kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yaba wa mambobin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suka bai wa ziyarar Makinde a Arewa maso Gabas.

Mohammed ya bayyana APM a matsayin jam’iyyar da za ta iya magance matsalolin Nijeriya, sannan ya buƙaci ’yan ƙasa su mara wa jam’iyyar da ’yan takararta baya a zaɓen 2027.

Shi ma ɗan takarar gwamnan Adamawa na APM, Abdulrahaman Haske, ya buƙaci shugabanni da mambobin jam’iyyar su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan masu zaɓe a jihohi, ƙananan hukumomi, mazabu da rumfunan zaɓe domin neman nasara a zaɓen mai zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata