DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, October 11, 2026
HomeLabaraiSERAP ta maka CBN a kotu kan $6.23m da N1.63trn na kuɗaɗen...

SERAP ta maka CBN a kotu kan $6.23m da N1.63trn na kuɗaɗen gwamnati

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar kare haƙƙin jama’a da riƙon amana ta maka Babban Bankin Nijeriya (CBN) a kotu, tana neman a tilasta masa yin bayani kan dala miliyan 6.23 da sama da Naira tiriliyan 1.63 na kuɗaɗen gwamnati da rahoton Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya ya nuna akwai tambayoyi kan yadda aka yi amfani da su.

Rahoton, wanda aka wallafa ranar 7 ga Agusta, 2026, ya yi nuni da wasu mu’amalolin kuɗi da basussukan da ba a karɓo ba a lokuta daban-daban tsakanin Janairu da Disamba 2023 kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2450/2026 da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Juma’ar da ta gabata, SERAP na neman umarnin kotu da zai tilasta wa CBN bayyana yadda aka fitar da kuɗaɗen, waɗanda suka amfana da su, matsayin biyan basussukan da kuma matakan da aka ɗauka wajen karɓo kuɗin.

Ƙungiyar ta kuma nemi CBN ya bayyana sakamakon binciken cikin gida da ya gudanar kan zargin damfarar kuɗin da aka ce an nema domin gudanar da zaɓe, tare da bayyana jami’an da suka amince da fitar da kuɗin da kuma matakan ladabtarwa da aka ɗauka.

Rahoton Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya ya nuna cewa dala miliyan 6.23 da ake magana a kai ta shafi wata buƙatar kuɗin zaɓe da ake zargin an yi ta da sunan tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

Rahoton ya ce sashen binciken cikin gida na CBN ya nuna cewa an kashe kuɗin ne bayan samun buƙatar, amma bankin bai bai wa masu binciken kuɗaɗen rahoton bincikensa domin tantancewa ba. Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya ya nuna damuwa kan yiwuwar asarar kuɗin ta hanyar biyan kuɗaɗen da ba su dace ba, tare da ba da shawarar a karɓo su a mayar da su baitulmalin gwamnati.

Baya ga wannan, rahoton ya nuna cewa akwai bashin tallafi na Naira tiriliyan 1.252 da aka bai wa gwamnatocin jihohi wanda ba a karɓo ba, da kuma Naira biliyan 116.18 na basussukan da aka bai wa bankunan da suka shiga matsala ko aka rushe.

Rahoton ya kuma ambaci Naira biliyan 262.86 da aka fitar ƙarƙashin shirin Anchor Borrowers’, wanda aka ƙaddamar domin tallafa wa manoma da ƙara samar da abinci. An nuna damuwa cewa wasu masu kula da shirin sun riƙe kuɗin, yayin da CBN bai gabatar da cikakken jerin waɗanda suka amfana ko hujjojin tasirin shirin ga samar da abinci ba.

SERAP ta kuma nemi kotu ta tilasta wa CBN yin bayani kan akwatuna bakwai na takardun kuɗi da ke jiran bincike, da motoci marasa amfani da aka bari a reshen bankin da ke Legas, da kuma motar jigilar kuɗi da ta lalace a reshen bankin da ke Abeokuta.

Ƙungiyar ta ce waɗannan batutuwa na haifar da tambayoyi kan yadda ake kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen gwamnati bisa ƙa’ida.

SERAP ta kafa ƙarar tata kan tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa gyara, da dokar CBN ta 2007, tare da wajibcin Nijeriya na yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙarƙashin yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da cin hanci.

Ta ce ’yancin cin gashin kan CBN ba ya keɓe bankin daga binciken kuɗaɗen gwamnati, buƙatar bayar da bayanan kuɗi ko binciken zarge-zargen almundahana.

Lauyoyin SERAP, Kolawole Oluwadare, Kehinde Oyewumi, Andrew Nwankwo da Kelechi Anwu, ne suka shigar da ƙarar a madadin ƙungiyar.

Ya zuwa lokacin da aka wallafa bayanin, ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata