Rundunar Sojin Nijeriya ta kuɓutar da mutane 26 da ake zargin waɗanda ake safarar mutane ne a Jihar Benue, tare da kuɓutar da wata mata da aka sace a Kogi da kuma kama wani da ake zargin shugaban ’yan ta’adda ne a Kaduna.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa waɗannan nasarorin sun samu ne a wasu samamen tsaro da sojoji suka gudanar a jihohi daban-daban ranar Juma’a da Asabar.
A Benue, dakarun Operation Whirl Stroke, tare da haɗin gwiwar ’yan sanda da jami’an sa-kai, sun kai samame kan wata ƙungiyar da ake zargin tana safarar mutane a Ƙaramar Hukumar Otukpo ranar Juma’a.
Rahoton ya ce sojojin sun kama wani mutum tare da kuɓutar da mutane 26, waɗanda aka miƙa wa ’yan sanda tare da wanda ake zargin domin ci gaba da bincike.
A Kaduna kuma, dakarun Operation Fansan Yamma sun kama wani mutum mai suna Yusuf Iliya San a Maraban Kakini ranar Asabar, bisa zargin yana jagorantar ’yan ta’adda da ke aikata laifuka a yankin Birnin Gwari.
Rahoton ya ce wanda ake zargin yana hannun sojoji domin ɗaukar matakan da suka dace. A wani samame na daban a yankin Dogon Dawa zuwa Takama da ke Birnin Gwari, sojoji sun fatattaki wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne bayan sun kai musu hari.
Maharan sun tsere, inda suka bar bindigar AK-47, harsasai 15, babura biyu da wayar hannu. Sai dai wani soja ya samu rauni, kuma an garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
A Jihar Kogi, dakarun Operation Whirl Stroke tare da jami’an tsaron daji sun kuɓutar da wata mata da aka yi garkuwa da ita a Ette, Ƙaramar Hukumar Olamaboro, ranar Juma’a. Masu garkuwar sun tsere bayan ganin sojojin, lamarin da ya ba da damar sake haɗa matar da iyalanta.
Sojojin sun kuma gano harsasai ta bindigar AK-47, harsasai 60 na musamman masu girman 7.62mm da wasu kayayyaki a wani samame da suka gudanar a hanyar Okene zuwa Okpella.
A Abia kuwa, sojoji tare da haɗin gwiwar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) sun kama mutane uku da ake zargin dillalan miyagun ƙwayoyi ne a Obehie, Ƙaramar Hukumar Ukwa West, ranar Juma’a. An miƙa waɗanda ake zargin da ƙwayoyin da aka ƙwato ga hukumar domin ci gaba da bincike.
A Filato, rahoton ya ce wani ɗan sa-kai ya mutu bayan wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe shi a ƙauyen Magi Mbar, Ƙaramar Hukumar Bokkos, ranar Juma’a.
Rahoton ya ƙara da cewa maharan sun tsere bayan ganin sojoji, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafke su.
