Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaZaben Okowa a matsayin abokin takarar Atiku ne kuskuren da ya kayar...

Zaben Okowa a matsayin abokin takarar Atiku ne kuskuren da ya kayar da PDP a 2023 — Abba Moro

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ya bayyana cewa zaɓen tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, babban kuskure ne da ya haifar da faduwar jam’iyyar.

Sanata Moro ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Channels TV, inda ya mayar da martani kan kalaman Okowa da ya ce yana nadamar karɓar matsayin mataimakin Atiku. A cewar Sanata Moro, wannan furuci na Okowa bai dace ba, musamman da yake cewa shi da kansa ya nemi matsayin ba wani ya tilasta masa ba.

A cewarsa, akwai wasu fitattun ‘yan jam’iyyar PDP daga kudu da suka fi cancanta kuma da za su iya jawo ƙuri’u, idan aka zaɓe su maimakon Okowa. Ya kuma ce rashin samun nasara a jiharsa da kuma gaza kawo ƙuri’u daga Delta na nuna rashin karɓuwarsa a tsakanin jama’a.

Sanata Moro ya ƙara da cewa jam’iyyar PDP na da ƙwarin gwiwar sake dawowa da ƙarfin gwiwa gabanin zaɓen 2027, inda ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar daga jihohi 36 da Abuja, sun gana kwanan nan domin tsara yadda za a farfaɗo da jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata