Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Alhamis, 14 ga Agusta, domin ziyarar kasashe biyu – Japan da Brazil.
Shugaban kasar zai tsaya a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa kafin ya ci gaba zuwa Japan.
A Japan, Shugaba Tinubu zai halarci taron Tokyo International Conference on African Development karo na tara (TICAD9), wanda zai gudana a birnin Yokohama daga 20 zuwa 22 ga watan Agusta.
Taron na bana zai tattauna hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Afrika da inganta yanayin kasuwanci ta hanyar zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu da kirkire-kirkire.
Har ila yau, taron zai mayar da hankali kan gina Afrika mai dorewa da kwanciyar hankali.
Bayan kammala taron TICAD9, Shugaba Tinubu zai tafi birnin Brasilia, babban birnin kasar Brazil, daga Lahadi, 24 ga Agusta zuwa Litinin, 25 ga Agusta, a wata ziyarar kwana biyu bisa gayyatar shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva.
A yayin wannan ziyara, Shugaba Tinubu zai gana da takwaransa na Brazil tare da halartar taron kasuwanci da ’yan kasuwa.
Tawagarsa za ta hada da ministoci da jami’an gwamnati masu ruwa da tsaki, domin kara karfafa hadin gwiwa da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da takardun fahimtar juna tsakanin Najeriya da Brazil.



