Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirinsa na tura sabbin kayan yaƙi na zamani da amfani da fasaha zuwa jihar Katsina domin kawo karshen matsalar da ke addabar jihar.
Tinubu ya sanar da hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar ’yan jihar karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda a fadar sa da ke Abuja.
Ya ce wajibi ne a shawo kan kalubalen yana mai umartar hukumomin tsaro su ƙara himma tare da samar da karin jiragen leƙen asiri domin yaki da ‘yan ta’addan.
Shugaban ya kuma bayyana cewa daga yanzu yana buƙatar samun rahoton ayyukan soji a Katsina kullum, tare da jaddada cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.



