Gwamnatin tarayyar Nijeriya na shirin sake ciyo bashin dala biliyan 1.75 daga bankin duniya duk da samun karuwa a kudaden shiga da kaso 40 a cikin watanni takwas na shekarar 2025, kamar yadda binciken jaridar punch ya nuna.
A ranar Laraba fadar shugaban Najeriyar ta bayyana ci gaban da ta ce ta samu a kudaden shiga daga bangarorin da ba na man fetur ba.
Sai dai binciken na Punch ya bayyana cewa akwai wuraren muhimman ayyuka da ke bukatar a cike musu gibi, musamman ayyukan gine-gine, bayan da kungiyar ‘yan kwangila’ yan asalin Najeriya suka gudanar da zanga-zangar neman a biya su basukan da suke bi tun shekarar 2024, wanda adadin su ya doshi Naira Tiriliyan 4.
