Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya ta ce za ta fara bayyana sunayen kamfanonin da ke karya ka’idojinta, musamman kan jinkirin tashi da kuma dakatarwa.
Cikin wani gargadi da ya wallafa a shafinsa na X, mai magana da yawun hukumar Michael Achimugu, ya ce duk wani fasinja da ya gamu da jinkiri ko dakatarwar tashin jirgi daga karfe goma na dare zuwa hudu na asuba, to wajibi ne kamfanin ya tanadar masa da wurin kwana a otal.
Wannan ya zo ne bayan da ake samun yawaitar korafi daga fasinjoji kan irin kalubalen da suke fuskanta yayin tashi ko saukar jiragen sama, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Sai dai hukumar ta ce daukar wannan mataki zai taimaka matuka wajen inganta harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya.
