Gwamnatin Jihar Kano ta umarci hukumar Hisbah da ta fara shirin daura aure ga mutane 2,000 a karkashin shirin gwamnati na auren gangami da aka tsara.
Mataimakin kwamandan hukumar, Sheikh Mujahid Aminudeen, ya shaida wa jaridar Punch a ranar Alhamis cewa za a fara shirye-shiryen bikin nan ba da jimawa ba.
Ya bayyana cewa dukkan ma’auratan da suka yi rajista dole ne su yi gwajin lafiya, ciki har da cuta mai karya garkuwar jiki HIV/AIDS, Hepatitis, gwajin jini da kuma na shaye-shaye kafin a amince da su.
A cewarsa, an dawo da tsarin ne domin tallafa wa zawarawa, ‘yan mata da samari marasa galihu, tare da rage yawaitar munanan dabi’u da matsalolin zamantakewa a cikin al’umma.
