Ƙwararrun likitocin mata sun gargaɗi mata da ’yan mata game da amfani da takardar goge baki (tissue paper), auduga, ko tsummoki a matsayin madadin audugar tsafta ta al’ada, suna masu jaddada cewa yin hakan na iya jawo ƙaiƙayin fata, cututtukan sanyi na gaba, toshewar magudanar kwayayen halitta, da kuma matsalar rashin haihuwa a nan gaba.
A zantawarsu da sashen lafiya na jaridar Punch, likitocin sun bayyana cewa amfani da “tissue” ya fi kowanne haɗari saboda takardar tana rubecewa tare da kakkaryewa idan ta ji ruwa ko jini. Ɓangarorin takardar da suka rage a jiki na iya zama kamar wani baƙon abu a cikin gaban mace, wanda zai iya jawo wari, kumburi, da kuma ƙwayoyin cuta masu haɗari.
Wani Farfesa a fannin lafiyar mata da haihuwa a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, Abubakar Panti, wanda kuma babban likita ne a Asibitin Koyarwa na jami’ar (UDUTH), ya bayyana cewa auduga ko takardar “tissue” ba ingantattun kayan da aka amince a yi amfani da su ba ne a likitance lokacin al’ada.
Farfesa Panti ya ce, “Takardar ’tissue’ na iya zama babban ƙalubale domin an yi ta ne domin ta narke idan ta jiƙa. Tana jiƙewa da sauri, ta karye, sannan ɓangarorinta su maƙale a fata ko su shiga cikin farji. Waɗannan ɓangarori na iya jawo ruwa mai wari da kuma kumburin farji.”
Ya kuma yi gargaɗi mai ƙarfi kan tura auduga ko “tissue” a cikin farji domin tsayar da jini, yana mai cewa yin hakan na janyo mummunar kamuwa da cuta.
Farfesa Panti ya bayyana cewa duk da cewa ƙaiƙayi ko ƙaiƙayin fata a lokacin al’ada ba lallai yana nufin kamuwa da cuta ba—domin wani lokacin kan iya kasancewa rashin dacewar audugar al’adar da fata —amma bai kamata mata su yi watsi da waɗannan alamomin ba. Ya buƙaci mata masu fama da ƙaiƙayi su sauya zuwa audugar da ba ta da kamshi daga wasu kamfanonin, ko kuma su yi amfani da sauran ingantattun kayan da aka ƙera na musamman don al’ada kamar kofin al’ada ko gajeren wandon al’ada.
A nasa ɓangaren, wani fitaccen Farfesa a fannin lafiyar mata, Oladapo Ladipo, ya gargaɗi ‘yan mata cewa cututtukan da ake samu daga rashin ingantaccen tsarin tsaftar al’ada na iya hayewa zuwa sama a cikin mahaifa.
“Idan cuta ta shiga cikin mahaifa, za ta iya toshe magudanar ƙwai biyu. Idan hakan ta faru, za su fuskanci matsalar rashin haihuwa a gaba idan sun girma suka yi aure. Saboda haka akwai buƙatar a guji amfani da tsummoki da ’tissue’,” in ji Farfesa Ladipo.
Shi ma wani kwararren likitan mata a Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Asaba, Dokta Daniel Adegbulu, ya bayyana cewa yawancin takardun “tissue” ana yin su ne daga dattin takardu da aka sake sarrafawa, don haka amfani da su a wurare masu laushi na jiki na da matuƙar haɗari ga lafiyar mata.
