Jihar Kano ta sake zama zakara a jarrabawar kammala sakandare ta Hukumar Jarrabawa ta Ƙasa (NECO) ta shekarar 2026, inda ɗalibai 74,413 suka samu nasarar samun maki biyar (credits) ciki har da yaren Turanci da Lissafi.
Sakamakon ya nuna cewa Jihar Legas ce ta zo ta biyu da ɗalibai 72,496, yayin da Jihar Oyo ta zo ta uku da ɗalibai 55,543, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Wannan nasara ta sa Jihar Kano ta riƙe matsayi na ɗaya a jere har sau biyu, bayan ita ce ta zo ta farko a jarrabawar NECO ta shekarar 2025 da mafi yawan ɗaliban da suka samu maki biyar ciki har da Turanci da Lissafi.
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar a Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya ɗalibai, malamai, iyaye, da sauran masu ruwa da tsaki murna kan wannan babban ƙoƙari.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan nasara a jere shaida ce da ke nuna cewa zuba jarin da gwamnatinsa ke yi a fannin ilimi yana haifar da kyakkyawan sakamako a ƙasa.
A cewarsa, “Kano ta riƙe matsayi na ɗaya a NECO sau biyu a jere, lamarin da ya mai da jihar a matsayin wadda ta fi kowace jiha bajinta a jarrabawar SSCE a shekaru biyu a jere (2025 da 2026).”
Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba fannin ilimi fifiko ta hanyar ƙara kasafin kuɗi, inganta kayan aiki a makarantu, ɗaukar sababbin malamai da horar da su, bayar da tallafin karatu, da kuma tallafa wa ɗalibai marasa galihu.
Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati, ta kashe sama da naira biliyan 4.4 a shekarar 2026 wajen biya wa ɗalibai kuɗin jarrabawar SSCE, musamman ɗaliban da suka fito daga gidajen marasa ƙarfi, domin cire shingen kuɗi da ba su damar rubuta jarrabawa a yanayi mai kyau.
Sanarwar ta ƙara da cewa fannin ilimi ya ci gaba da karɓar kaso mafi tsoka a kasafin kuɗin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Yusuf, wanda ya zarce ma’aunin da hukumar UNESCO ta gindaya.
A shekarar 2024, ilimi ya samu kaso 29.95 na kasafin kuɗin jihar. A shekarar 2025 kuma an ƙara shi zuwa naira biliyan 168.35, wato kashi 31 na kasafin. A shekarar 2026 kuma, jihar ta ware naira biliyan 405.35 ga fannin ilimi, wanda ke wakiltar kusan kashi 30 na jimillar kasafin kuɗin jihar na sama da naira tiriliyan 1.478.
Gwamnan ya jaddada cewa zuba jarin ya haɗa da gyaran azuzuwa, ɗaukar malamai, samar da kayan karatu, kayan makaranta, da tallafin karatu domin gina tsarin ilimi mai inganci ga matasan Kano.
