Rundunar jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta sanar da cikakkiyar biyayyarta ga ƙungiyar “Rainbow Coalition”, wadda Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kafa gabanin babban zaɓen 2027.
Ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Dokta David Ombugadu, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a birnin Lafia, yayin buɗe yaƙin neman zaɓensa a hukumance, taron da ya samu halartar masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam’iyyar daga ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ombugadu ya tabbatar da cewa mambobin PDP a Jihar Nasarawa sun amince da tafiyar Rainbow Coalition kuma za su kaɗa ƙuri’unsu ne bisa umarni da tsarin da Wike ya shimfiɗa.
Ombugadu ya ce, “Muna so mu tabbatar a yau cewa dukkan Jihar Nasarawa na tare da ƙungiyar Rainbow Coalition. Dukkanmu muna da haɗin kai wajen marawa shugabanmu na ƙasa baya, wato Ministan FCT, Nyesom Wike. Muna jiran shugabanmu na ƙasa ya nuna muna alkibla. Duk inda ya dosa, can za mu nufa.”
Ɗan takarar gwamnan ya buƙaci wakilan da suka zo daga Abuja da su isar da gaisuwar al’ummar Nasarawa ga Wike, wanda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai cike da ƙwarewa da basira. Ya ce al’ummar jihar na ɗokin ganin ya kawo ziyara jihar.
Da yake magana kan shirinsa idan aka zaɓe shi, Ombugadu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ba fannin tsaro, ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma shugabanci na bai ɗaya fifiko. Ya ƙara da cewa Jihar Nasarawa na da albarkatun ma’adanai kamar zinare, lithium, da wolframite, amma har yanzu al’umma ba su amfana da su ba yadda ya kamata, yana mai alƙawarin inganta kiwon lafiya da tsaro ga manoma.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban PDP na Ƙasa, Yusuf Agirikwe, ya bayyana cewa jam’iyyar na da goyon bayan jama’a na karɓar mulkin jihar a 2027, inda ya buƙaci magoya baya da su fito su kaɗa ƙuri’a tare da tsare ta domin tabbatar da nasara.
