Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiMasarautar Kano ta yi rashin jigo a cikinta

Masarautar Kano ta yi rashin jigo a cikinta

Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma dan majalisar masarautar Kano, Sheikh Kabiru Ibrahim Babban Malami Madabo, ya rasu da yammacin Alhamis a gidansa da ke unguwar Madabo a Kano bayan fama da gajeriyar jinya.

Daily Trust ta ruwaito Sheikh Kabiru wanda ya rasu yana da shekaru 85, ya bar mata uku da ’ya’ya 26 da jikoki da dama.

Kafin rasuwarsa, Sheikh Kabiru ya kasance jigo a majalisar masarautar Kano, inda yake ba da shawara kan ilimin Fiqihu da aiwatar da dokokin Musulunci a rayuwar yau da kullum.

An gudanar da sallar jana’izarsa da misalin ƙarfe 10 na safiya a fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata