Home Labarai Buhari ya amince da ƙudirin dokar ƴan sanda ta 2020

Buhari ya amince da ƙudirin dokar ƴan sanda ta 2020

143
1

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu ga ƙudirin dokar ƴan sanda ta shekarar 2020 zuwa doka.

Mai taimaka wa Shugaban ƙasar na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Adesina ya ce Buhari ya amince da ƙudirin ne a cikin wata takarda da ya aike wa majalisar ƙasar ta hannun akawun majalisar, mai ɗauke da kwanan watan 16 ga watan Satumba, 2020.

Sanarwa ta kuma ƙara da cewa sabuwar dokar, gyara ne ga dokar shekarar 2004, wadda za ta ƙara samar da kyakkyawan tsari ga aikin da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da ayyuka da dukiyar ƴan sandan.

1 COMMENT

Leave a Reply