Wata kotun majistire da ke birnin Chester a Birtaniya ta yanke wa wani dan Nijeriya hukuncin zaman gidan yari na tsawon makonni 16, bayan samun sa da laifin yi wa wata ma’aikaciyar jinya sojan gona.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, dan Nijeriyar mai suna Lucius Njoku ya gudanar da aiki a tsakanin watannin Fabarairu da Afrilun 2024, a sashen hadura da bayar da kulawar gaggawa na asibitin Chester da ke yankin Cheshire.
Masu gabatar da kara, sun bayyana wa kotun cewa mutumin ya yi aiki ne da sahalewar ma’aikaciyar jinyar mai suna Joyce George wacce ta kasance ‘yar Nijeriya ita ma, inda ya riƙa amfani da katin shaidar ta.
Sai dai mahukunta ce lamarin abin damuwa ne, duk da cewa ba a samu wata matsala a tsawon lokacin da ya gudanar da aikin ba.
Kotun dai ta tuhumi ma’aikaciyar jinyar da damfara, sai dai bayan gudanar da bincike an samu cewa ta cika wandonta da iska, lamarin da ya sa kotu ta bayar da umarnin a nemo tare da gurfanar da ita.
