DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar wakilan Nijeriya ta amince wa Tinubu ya ciyo bashin dala biliyan 2.35

-

Majalisar wakilai ta Nijeriya ta amince da bukatar shugaban Tinubu na neman bashin dala biliyan 2.347 daga ƙasashen waje domin cike gibin kasafin kuɗin 2025 da kuma sake biyan wani tsohon bashin a Eurobond.

An amince da bukatar ne bayan rahoton kwamitin Majalisa kan tallafi da harkokin basussuka da shugaban kwamitin, Ɗan majalisa Abubakar Hassan Nalaraba, ya gabatar a zaman majalisar da kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya jagoranta.

Google search engine

Jaridar Punch ta rawaito cewa tun bayan da shugaba Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023, gwamnatinsa ta karɓi basussuka da dama domin tallafa wa shirin gwamnati da ayyukan ci gaba.

A cikin shekaru biyu, Nijeriya ta karɓi sama da dala biliyan 7.2 daga bankin duniya da kuma bashin dala biliyan 1 daga bankin raya Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Nijar da Chadi na son karfafa dangantakarsu

Kasashen Nijar da Chadi sun kammala wani taron hadin gwiwa na kwanaki biyu da suka gudanar a birnin N'djamena na kasar Chadi karkashin jagorancin Firaministocin...

Matsalar Nijeriya ba ta addini ba ce illa rashin shugabanci nagari – Sowore

Dan gwagwarmayar kare hakkin dan’Adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka, Donald Trump da ya...

Mafi Shahara