Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, na shirin yin murabus daga mukaminsa bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Kamar yadda sanarwar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Tunji Bolaji, ta bayyana, an tabbatar da wannan mataki ne bayan ganawar sirri da aka yi a ranar Talata.
Rahotanni sun nuna cewa Adelabu ya gabatar da cikakken bayani kan ayyukan da ya gudanar a fannin wutar lantarki, ciki har da manufofin inganta samar da wuta da kuma ƙarfafa tsarin rarraba ta a ƙasar.
Ana sa ran ministan zai ajiye mukaminsa nan da kwanaki masu zuwa domin tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027.
