Shugaban kamfanin Karex, wanda shi ne mafi girma a duniya wajen kera kwaroron-roba, da ke ba da kariya wajen daukar cutukan da ke da nasaba da jima’i ya ce kamfanin na shirin ƙara farashin kayayyakinsa da kashi 30 cikin 100 ko ma fiye da haka, idan har rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya ci gaba da kawo cikas ga samar da kayan da ake amfani da su wajen ƙera kayayyakin.
Babban daraktan kamfanin, Goh Miah Kiat, ya bayyana wa kafafen yaɗa labarai cewa farashin samar da kayayyaki ya tashi sosai tun bayan fara rikicin.
Kamfanin mai hedikwata a Malaysia yana samar da fiye da biliyan biyar na kwaroron roba a kowace shekara, inda yake samar da su ga manyan kamfanoni a duniya kamar Durex da Trojan, har ma da tsarin kiwon lafiya na ƙasashe irin su National Health Service a Birtaniya.
