DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, September 18, 2026
HomeSiyasaAlhakin yaran da ke fama da matsananciyar yunwa a Nijeriya na wuyan...

Alhakin yaran da ke fama da matsananciyar yunwa a Nijeriya na wuyan gwamnatin Tinubu – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya ce matsalar tsadar rayuwa a Nijeriya na ƙara jefa iyalai cikin halin da ba sa iya samar da ingantaccen abinci ga ’ya’yansu, lamarin da ya ce ke barazana ga lafiyar yara da makomar ƙasar.

Atiku ya yi wannan jawabi ne yayin da sabbin alkaluman abinci mai gina jiki suka nuna cewa kashi 41.1 cikin 100 na yaran ƙasa da shekaru biyar na fama da ƙarancin tsayi sakamakon rashin isasshen abinci mai gina jiki, yayin da adadin ya kai kashi 58.2 a yankin Arewa maso Yamma.

Atiku, a cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, ya ce tsadar abinci, sufuri da makamashi na ƙara matsa wa iyalan Nijeriya lamba, yana mai cewa yaro ba ya fahimtar alkaluman hauhawar farashi, sai dai ya san ko akwai abinci a kan tebur.

Ya ce idan abinci mai gina jiki ya gagari iyalai, illar hakan za ta bayyana a lafiyar yara, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce tsadar man fetur na ƙara jawo hauhawar farashin kayayyaki, tun daga jigilar amfanin gona daga gonaki zuwa kasuwanni har zuwa sufuri da harkokin ƙananan sana’o’i.

Ya bayyana cewa shirin tallafin man fetur da yake gabatarwa ba wai komawa tsarin tallafawa man fetur da ake shigowa da shi ba ne, sai dai tallafin da zai kasance ga man da aka tace a cikin Nijeriya, tare da iyakance shi, sanya shi cikin kasafin kuɗi da kuma gudanar da bincike kan saɓani da almundahanar da ake zargi.

Atiku ya ce manufarsa ita ce rage kuɗin samar da makamashi, da sufuri, tare da ƙarfafa noma da masana’antu domin rage nauyin da ke kan talakawa.

Ya ce ya kamata manufofin tattalin arziki su mayar da hankali kan ko talaka zai iya biyan kuɗin abinci da sauran bukatun yau da kullum, musamman ganin yadda matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ke ƙara kamari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata