DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, September 18, 2026
HomeSiyasaAtiku bai kamata ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba -...

Atiku bai kamata ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba – Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bai kamata ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba.

Gidan talabijin na TVC News ya ruwaito Sani ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a kafar sada zumunta ranar Alhamis, yayin da yake tsokaci kan batun rabon madafun iko tsakanin Arewa da Kudu.

A cewarsa, takarar shugaban ƙasa a 2027 ya kamata ta kasance tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi, Omoyele Sowore, Seyi Makinde, Adewole Adebayo, Donald Duke da sauran ’yan takarar daga Kudancin Nijeriya.

Tsohon ɗan majalisar ya ce Kudancin Nijeriya ya kamata ya kammala wa’adin shekaru takwas kafin a mayar da mulki Arewa a shekarar 2031.

Ya amince cewa tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu ba tanadi ba ne da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya shimfiɗa, amma ya ce tsarin ya dace da adalci da yanayin siyasar ƙasar.

Sani ya ce bai kamata a yi watsi da abubuwan da suka shafi tarihin siyasar Nijeriya da tsarin da aka saba bi wajen rabon mulki ba, yana mai cewa ya kamata a duba waɗannan abubuwa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Ya kuma yi gargadin cewa waɗanda ke cewa bai kamata a mutunta tsarin rabon mulki a 2027 ba, kada su yi tsammanin za a mutunta shi a 2031, lokacin da ya ce arewa za ta nemi damar komawa kan kujerar shugaban ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata