Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya fayyace kalamansa kan gwamnonin Arewa da suka goyi bayan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa maganar gwamnonin shida ta shafi lokacin shawarwari da ƙawancen siyasa ne kafin zaɓen fidda gwani na APC a watan Yunin 2022.
Jaridar Punch ta ruwaito Shettima ya bayyana hakan ne ranar Laraba a fadar Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari, yayin bikin naɗa Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, sarautar Sardaunan Masarautar Ilorin.
Ya ce daga cikin jihohin Arewa 19, gwamnonin shida ne suka amince da Tinubu tare da mara masa baya a wancan lokaci.
Ya bayyana tsohon Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, da Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a matsayin biyu daga cikin gwamnonin shida, amma ya ƙi bayyana sunayen sauran huɗun, yana mai cewa hakan na iya haifar da cece-ku-ce.
Sai dai a wata sanarwa da Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da sadarwa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, ya fitar ranar Alhamis, an ce ba yana nufin cewa gwamnonin APC na Arewa ba su goyi bayan Tinubu ba bayan ya samu tikitin jam’iyyar.
Nkwocha ya ce bayan kammala zaɓen fidda gwani, gwamnonin APC na Arewa sun haɗa kai wajen mara wa Tinubu baya, tare da taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓen da ya kai ga nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ofishin mataimakin shugaban ƙasar ya ce Shettima na mutunta gwamnonin Arewa da sauran shugabannin APC, tare da amincewa da gudunmawar da suka bayar wajen nasarar jam’iyyar da kuma Tinubu.
Nkwocha ya ƙara da cewa Shettima ya yi nadamar duk wata fassara da za ta nuna cewa kalamansa na nufin ya rage darajar gudunmawar gwamnonin Arewa, yana mai cewa bayanin ya fito ne domin sanya maganar cikin ainihin mahallin da aka yi ta.
