Sarkin Ife, Mai Martaba Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, ya jinjina wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan rashin tsoma baki a cikin harkokin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), yana mai bayyana cewa irin wannan mataki na ƙara ƙarfafa gwiwar al’umma da amincewarsu ga tsarin dimokuraɗiyya.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Ooni ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yaɗa labarai na fadarsa, Sodiq Lawal, ya fitar a madadin daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Otunba Moses Olafare, a daidai lokacin da basaraken ya fara killace kansa na kwanaki bakwai domin gudanar da ibada kafin bikin al’adu na Olojo na shekarar 2026 a Ile-Ife da ke jihar Osun.
Wannan keɓewa da basaraken ya fara a yammacin ranar Lahadi na daga cikin al’adun gargajiya da ke share fage ga bikin Olojo na shekara-shekara, wanda ke ɗaya daga cikin muhimman bukukuwan al’adun Yarbawa da aka sani a Ile-Ife.
Da yake magana jim kaɗan kafin shiga keɓewar, Ooni, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Nijeriya (NCTRN), ya bayyana cewa Nijeriya ta fi ƙarfin muradun kowane ɗan siyasa, don haka ya buƙaci shugabannin siyasa da su tabbatar bambance-bambancensu ba su zubar da mutuncin ƙasar ko kawo barazana ga haɗin kanta ba.
Basaraken ya kuma yaba wa al’ummar jihar Osun kan yadda suka gudanar da zaɓen gwamnan jihar da aka kammala, yana mai bayyana sakamakon a matsayin shaida ta ikon da ‘yan ƙasa ke da shi na zaɓar shugabanninsu ta hanyar ƙuri’a. Ya buƙaci tsarin zaɓen ya ci gaba da bai wa ‘yan Nijeriya ‘yancin yin zaɓinsu ba tare da tsoro ba.
Ooni ya ƙara da cewa addu’o’in da zai yi a cikin kwanaki bakwai na keɓewar za su shafi tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar, musamman yayin da Nijeriya ke shirin fuskantar babban zaɓe na gaba. Ya yi kira ga ‘yan siyasa da su sanya jin daɗin rayuwar talakawa a gaba maimakon saɓanin siyasa, tare da guje wa furucin da zai raba kan al’umma domin mulki na wucin-gadi ne.
Basaraken ya bayyana cewa wannan keɓewa ta kwanaki bakwai za ta ba shi damar sadarwa da kuma gudanar da al’adun da ke da alaƙa da bikin Olojo, ciki har da shirin sanya rawanin gargajiya na Aare wanda ake yi a kowace shekara.
