DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeBabban Labari An bukaci kotu ta hana Tinubu tsayawa takarar shugaban kasa a zaben...

An bukaci kotu ta hana Tinubu tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027

An shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano domin neman a hana Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027, bisa zargin gabatar da takardun shaidar karatu na bogi da kuma takardar kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC) da ake zargin bata da inganci.

Masu karar, cibiyar Centre for Reform and Public Advocacy (CFRPA), sun shigar da karar ne a gaban kotu, inda suka sanya Shugaba Bola Ahmed Tinubu, hukumar zaben Nijeriya INEC da kuma Jami’ar Chicago State University ta Amurka a matsayin wadanda ake kara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar a takardun karar mai lamba FHC/K/CS/312/2026, masu karar sun yi zargin cewa Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC takardar shaidar karatu daga Chicago State University da kuma takardar NYSC da suke ikirarin cewa ba su inganci lokacin zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Masu karar sun kuma yi zargin cewa Tinubu bai taba halartar Government College Lagos kamar yadda aka bayyana ba, suna masu cewa an kafa makarantar ne a shekarar 1974, alhali ana ikirarin ya kammala karatu tun kafin wannan lokaci.

Haka kuma, sun ce shugaban kasar ba shi da ingantacciyar takardar kammala makarantar sakandare, wadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada a matsayin mafi karancin sharadin neman takarar shugaban kasa.

CFRPA ta bayyana cewa ta rubuta wa INEC wasika tun ranar 19 ga Yunin 2026, tana neman hukumar ta yi karin haske kan cancantar Tinubu, amma ta ce har yanzu hukumar ba ta dauki wani mataki ba.

Masu karar sun kuma jingina hujjojinsu da hukuncin wata kotu a Amurka da aka yanke a shekarar 2023 a shari’ar In Re: Application of Atiku Abubakar, wanda ya tilasta wa Chicago State University sakin bayanan karatun Tinubu.

Sun yi ikirarin cewa bayanan da jami’ar ta fitar sun kunshi sabani da kuma wasu bayanai da suka hada da takardar shaidar Cambridge General Certificate of Education da suke zargin ta bogi ce.

A cikin bukatun da suka gabatar gaban kotu, CFRPA ta bukaci a ayyana cewa takardar shaidar Chicago State University da Tinubu ya gabatar ta bogi ce, sannan a umarci INEC ta hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Har ila yau, sun bukaci kotu ta umurci Chicago State University ta cire sunan Tinubu daga bayananta, tare da hana INEC saka sunansa cikin jerin ‘yan takarar shugaban kasa idan aka bude rajistar ‘yan takara.

Masu karar sun kuma mika takardun shaidu da wasiku da suka aikewa hukumar NYSC da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, inda suka bukaci hukumomin su bayyana matsayinsu kan takardar shaidar NYSC da ake zargin ta bogi ce.

Har zuwa lokacin buga wannan labari, babu wata sanarwa daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, INEC ko Chicago State University da ta mayar da martani kan karar da aka shigar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata