Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa da dawo da zaman lafiya da tsaro a ƙasar idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Atiku, wanda ke neman shugabancin ƙasar ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya kuma buƙaci masu zaɓe su karɓi katunan zaɓensu na dindindin (PVC).
Atiku ya nuna damuwarsa kan matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro da suka addabi al’ummar Nijeriya, yana mai cewa mutane daga shekaru daban-daban na fuskantar ƙalubalen rayuwa.
Ya ce iyaye da dama na cikin damuwa kan yadda za su samar wa ’ya’yansu abinci, yayin da wasu ’yan fansho ke fuskantar wahala tsakanin sayen abinci da kuma sayen magungunan da suke buƙata.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa matasa da ma’aikata na shan wahala wajen biyan buƙatun yau da kullum, duk da ƙoƙarin da suke yi wajen neman kuɗi.
A cewarsa, kuɗin sufuri, haya da sauran muhimman buƙatun rayuwa na cinye mafi yawan kuɗin da mutane ke samu, lamarin da ke ƙara musu matsin tattalin arziki.
A cewarsa, kuɗin sufuri, haya da sauran muhimman buƙatun rayuwa na cinye mafi yawan kuɗin da mutane ke samu, lamarin da ke ƙara musu matsin tattalin arziki.
Atiku ya kuma nuna damuwa kan matsalolin garkuwa da mutane da hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar, yana mai cewa iyalai da dama na rayuwa cikin fargabar tsaron ’yan uwansu.
Ya ce bai kamata iyalai su riƙa fuskantar yunwa da rashin tsaro a lokaci guda ba, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a bar waɗannan matsaloli su zama makomar ’ya’yan Nijeriya ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira ga dukkan masu zaɓen da suka yi rajista da su karɓi katunan zaɓensu na dindindin tare da adana su domin amfani da su a zaɓe mai zuwa.
