Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, zai kasance abokin tafiya a gwamnatinsa idan suka yi nasara a zaɓen 2027, ba kamar mataimakan shugaban ƙasa da ake warewa a matsayin ƴan kallo ba.
Obi ya bayyana hakan ne ranar Asabar bayan karɓar tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, inda ya kuma sanar da Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.
Kamar yadda Channels ya ruwaito, Obi ya ce gwamnatinsa za ta kasance mai haɗin kai da tuntuba, wadda mataimakin shugaban ƙasa ba zai zama “spare tyre” ba, sai dai cikakken abokin aiki wajen tafiyar da harkokin ƙasa.
Obi ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagora mai muhimmanci wanda ke da irin manufofinsa musamman a fannonin ilimi da tsaro. Ya ce za su yi aiki tare domin magance matsalolin da suka addabi Nijeriya.
Ya kuma jaddada cewa tsaro zai kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta bai wa fifiko, yana mai cewa babu wata ƙasa da za ta ci gaba idan al’ummarta na rayuwa cikin fargaba.
Ya ƙara da cewa burinsu shi ne gina Nijeriya mai haɗin kai da ƙarfafa cibiyoyin gwamnati domin samar da ci gaba mai ɗorewa.
