DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeLabaraiBabu kalaman da za su iya tausasa zukatan iyalan waɗanda suka rasa...

Babu kalaman da za su iya tausasa zukatan iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwansu a hatsarin NAF — Atiku

Ɗan takarar shugabancij Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya jajanta wa iyalan mutane 25 da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin saman rundunar sojin sama ta Nijeriya (NAF) da ya faru a jihar Ondo.

Atiku ya bayyana hatsarin a matsayin abu mai matuƙar tayar da hankali, inda ya aika da ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu, rundunar sojin sama da kuma rundunar sojin Nijeriya baki ɗaya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da aka tabbatar a ranar Talata, inda ya ce babu kalaman da za su iya kwantar da hankalin iyalan da wannan rashi ya shafa.

Ɗan takarar shugabancin kasar ya ce abin da ya faru ya fi ciwo musamman ga iyalan da suka rasa ’yan uwansu, ciki har da iyalan sojoji da sauran fasinjojin da ke cikin jirgin.

Ya ce hatsarin ya yi sanadiyyar rasa rayukan jami’an sama, sojoji da kuma wasu ’yan uwa, waɗanda suka bar gida domin gudanar da ayyukansu, amma suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari.

Atiku ya ce tunaninsa da addu’o’insa suna tare da iyalan dukkan waɗanda suka mutu, yana mai cewa iyayen da suka rasa ’ya’yansu, da ’ya’yan da suka rasa iyayensu, za su fuskanci babban gibi da radadin rashin da ba kalmomi za su iya bayyana shi ba.

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga rundunar sojin sama ta Nijeriya da rundunar sojin Nijeriya, tare da gwamnatin tarayya da al’ummar Nijeriya da kuma jihar Ondo.

Hatsarin ya faru ne a yankin Igbokoda da ke ƙaramar hukumar Ilaje a jihar Ondo, inda jirgin saman NAF mai lamba NAF 931 ya yi hatsari yayin da yake kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas.

Rundunar sojin sama ta tabbatar da cewa dukkan mutane 25 da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu, ciki har da ma’aikatan jirgin guda biyar da fasinjoji 20.

Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa Labarai na rundunar sojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya tabbatar da adadin mutanen da ke cikin jirgin da kuma asarar rayukan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata