DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeLabaraiGwamna Dauda ya nemi a dakatar da ƙirƙirar sabbin jihohi a yanzu

Gwamna Dauda ya nemi a dakatar da ƙirƙirar sabbin jihohi a yanzu

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta dakatar da batun ƙirƙirar sabbin jihohi a yanzu, yana mai cewa ya kamata a fara ƙarfafa jihohi 36 da ake da su kafin a ƙara samar da wasu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamna Lawal ya bayyana hakan ne a Gusau yayin wata ganawa da shugabannin kafafen yaɗa labarai, a wani ɓangare na bikin cika shekaru 30 da ƙirƙirar jihar Zamfara.

Gwamnan ya ce matsalolin kuɗaɗen da yawancin jihohin Nijeriya ke fuskanta a yanzu sun sa ya zama dole a sake duba batun ƙirƙirar wasu jihohin zai iya kawo ci gaban da ake fata.

Ya bayyana cewa ƙirƙirar jihohi a baya ya taimaka wajen kusantar da gwamnati ga al’umma, tare da samar da ayyukan yi da bunƙasa garuruwa.

Sai dai ya ce yanayin da ake ciki a Nijeriya a yanzu ya bambanta da wanda aka samu shekaru da dama da suka gabata, saboda wasu daga cikin jihohin da aka riga aka ƙirƙira na fuskantar matsalar kuɗin tafiyar da ayyukansu yadda ya kamata.

A cewarsa, kafin a fara neman ƙirƙirar wasu jihohi, ya kamata a fara tabbatar da cewa jihohin da ake da su suna da ƙarfin tattalin arziki da na gudanar da mulki da zai ba su damar biyan buƙatun jama’arsu.

Gwamna Lawal ya ce batun ƙirƙirar sabbin jihohi na daga cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a yayin aikin sake duba kundin tsarin mulkin Nijeriya da ake gudanarwa a yanzu.

Ya ce majalisar wakilai ta karɓi buƙatun ƙirƙirar sabbin jihohi guda 56 daga sassa daban-daban na ƙasar, amma waɗannan buƙatu na fuskantar matakai masu tsauri kafin su iya samun amincewar doka.

A ƙarƙashin sashe na 8 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999, ƙirƙirar sabuwar jiha na buƙatar cika wasu sharudda, ciki har da samun goyon bayan ’yan majalisun tarayya da na jihohin da abin ya shafa, ƙananan hukumomi da kuma gudanar da ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a.

Gwamnan ya ce duk da cewa ƙirƙirar Zamfara daga tsohuwar jihar Sakkwato a watan Oktoban 1996 ta kawo sauye-sauye masu amfani, bai kamata a yi amfani da wannan a matsayin dalilin ci gaba da raba jihohi ba tare da la’akari da yanayin tattalin arzikin da ake ciki ba.

Zamfara dai an ƙirƙire ta ne daga tsohuwar jihar Sakkwato a shekarar 1996 a lokacin mulkin soji na marigayi Janar Sani Abacha, inda aka sanya Gusau a matsayin babban birnin jihar.

Lawal ya ce tun bayan ƙirƙirar Zamfara, jihar ta samu damar kafa nata tsarin gudanar da mulki, tare da samun ci gaba a fannonin samar da ayyukan yi da bunƙasa birane, duk da cewa har yanzu akwai manyan ƙalubale.

Ya danganta ci gaban da jihar ta samu da irin salon shugabancin gwamnatocin da suka gabata, yana mai cewa kowace gwamnati ta zo da nata hanyoyin magance matsalolin jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatin da yake jagoranta na ƙoƙarin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar jihar, musamman a fannonin ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da noma.

Ya ce shirin gwamnatinsa na “Rescue Mission” ya ta’allaka ne kan muhimman fannoni shida, wato tsaro, ilimi, kiwon lafiya, noma, ababen more rayuwa da bunƙasa ɗan Adam.

A cewarsa, an samu ci gaba tsakanin kashi 60 zuwa 70 cikin 100 wajen aiwatar da manufofin da aka sanya a cikin wannan shiri.

Lawal ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin faɗaɗa tattalin arzikinta fiye da dogaro da noma kaɗai, ta hanyar amfani da albarkatun ma’adinan da jihar ke da su, musamman ma’adinai masu muhimmanci.

Gwamnan ya yi iƙirarin cewa Zamfara na kan gaba a Nijeriya wajen mallakar wasu daga cikin ma’adinai masu muhimmanci, yana mai cewa gwamnati ta gudanar da bincike tare da samun bayanan da suka tabbatar da hakan.

Ya ce inganta ababen more rayuwa da samar da yanayin da zai ƙarfafa zuba jari na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin sauya fasalin tattalin arzikin jihar da kuma inganta martabar Zamfara.

Gwamna Lawal ya ƙara jaddada cewa ya kamata a mayar da hankali wajen tabbatar da cewa jihohin da ake da su sun samu isasshen ƙarfin gudanar da ayyukansu da samar da ci gaba ga jama’a kafin a sake buɗe batun ƙirƙirar wasu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata