Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewa ba ta da hannu a wani zargin sammacin kama tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, dangane da binciken zargin batar da kudade har Naira tiriliyan 210.
Majalisar ta kuma yi suka kan kalaman Sanata Adams Oshiomhole da suka danganci lamarin, tana mai jaddada cewa duk wani mataki na hukuma dole ne ya bi ka’idoji da matakan da doka ta tanada.
Jaridar Punch ta ruwaito Sanatocin sun bayyana cewa babu wata sanarwa ko matsaya ta hukuma daga Majalisar Dattawa da ta amince da fitar da sammacin kama Kyari, tare da kira da a guji yada bayanan da ka iya haifar da rudani ga jama’a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
