Wata budurwa mai shekara 16 ta haifi jariri namiji, inda aka ce kakanta mai suna Musa Gado ne mahaifin yaron.
Jaridar Punch ta rawaito cewa an tabbatar da wannan zargi ne bayan an gudanar da gwajin DNA wanda ya nuna kakanta ne suka yi mu’amalar aure har hakan ta faru.
Bayan da yarinyar ta samu juna biyu, ana zargin kakanta ya shawo kanta da ta zubar da cikin. Ta yi kokarin yin hakan ta hanyar shan wasu magunguna da allurai, amma hakan bai yi nasara ba.
Daga bisani, yarinyar mai juna biyu ta kai rahoto ofishin Hukumar Kare Hakkin Yara, inda aka ajiye ta a karkashin kulawa har zuwa lokacin da ta haifi jaririn namiji.
