Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a 12, ga watan Yunin 2026, a matsayin ranar hutu ga ma’aikata da sauran al’umma domin bikin cika shekaru 27 da komawar ƙasar kan mulkin dimokuraɗiyya.
A wata sanarwa da babbar Sakatariyar a ma’aikatar harkokin cikin gida, Magdalene Ajani, ta fitar ta cewa hutun na daga cikin bukukuwan ranar Dimokuraɗiyya ta ƙasa.
Gwamnatin ta ce bikin na bana wata dama ce ta tunawa da irin gudunmawar da magabata da sauran masu fafutukar dimokuraɗiyya suka bayar wajen tabbatar da mulkin farar hula a Nijeriya.
