DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeKetareGwamnatin Nijeriya ta sake batar da ƙarin Naira miliyan 500 wajen karyata...

Gwamnatin Nijeriya ta sake batar da ƙarin Naira miliyan 500 wajen karyata zargin tsananta wa Kiristoci

Gwamnatin Nijeriya ta ɓatar da Naira miliyan 500 a shekarar 2025 wajen gudanar da wani kamfen na sadarwa na gaggawa da nufin karyata abin da ta bayyana a matsayin farfagandar ƙasashen Yamma kan zargin tsananta wa Kiristoci a Nijeriya.

Bayanan kashe kuɗin da aka samu a dandalin sa ido kan kashe kuɗin gwamnati na GovSpend sun nuna cewa an biya Naira miliyan 500 a ranar 19 ga Disamba, 2025, ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da sadarwa.

Jaridar Daily Trust ta ambato bayanin biyan kuɗin ya ce an ware kuɗin ne domin gabatar da hulɗa da kafafen yaɗa labarai na duniya don dakile abin da gwamnati ta kira haɗaɗɗiyar farfaganda daga ƙasashen Yamma kan zargin tsananta wa Kiristoci.

Wannan kashe kuɗi ya zo ne a shekarar da gwamnatin tarayya ta kuma ɗauki wani kamfanin hulɗa da gwamnati da masu tsara manufofi na Amurka aiki kan kwangilar dala miliyan tara, domin ƙarfafa hulɗar Nijeriya da jami’an Amurka kan zargin hare-haren da ake kai wa al’ummomin Kiristoci.

Takardun da aka shigar ƙarƙashin dokar Foreign Agents Registration Act (FARA) ta Amurka sun nuna cewa wani kamfanin lauyoyi mai suna Aster Legal da ke Kaduna ya ɗauki kamfanin DCI Group na Amurka aiki a madadin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, gwamnatin Nijeriya ta amince da biyan kamfanin dala 750,000 a duk wata, wanda ya kai dala miliyan tara a shekara idan aka sabunta kwangilar. An kuma tsara biyan dala miliyan 4.5 a matsayin kuɗin watanni shida na farko.

Matakin ya biyo bayan ƙara tsananta binciken da wasu ‘yan siyasa da jami’an Amurka ke yi kan rahotannin tashin hankalin da ya shafi al’ummomin Kiristoci a Nijeriya.

A watan Oktoban 2025, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargin suna fuskantar matsaloli masu tsanani kan ‘yancin addini.

Sai dai gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da cewa matsalar tsaro a ƙasar ta samo asali ne daga ta’addanci, ‘yan bindiga, rikice-rikicen al’umma da sauran laifuka, ba wai manufar tsananta wa wani addini ba, tana mai cewa Musulmi da Kiristoci duk suna cikin waɗanda tashe-tashen hankulan suka shafa.

Binciken bayanan Armed Conflict Location & Event Data (ACLED) ya nuna cewa Nijeriya ta samu rikice-rikicen tsaro 7,956 tsakanin Yuli 2025 da Yuni 2026, lamarin da ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 15,000 tare da jefa kimanin mutane miliyan 66.8 cikin barazanar tashin hankali da rashin tsaro.

Bayanan sun nuna cewa jihar Borno ce ta fi yawan rikice-rikicen 1,218, sai Katsina mai 958, Zamfara 885, Sokoto 599, Kaduna 390, Benue 377 da Filato 346.

Gwamnatin tarayya ta sha nanata cewa tana ƙoƙarin kawo ƙarshen ta’addanci da ‘yan bindiga, yayin da Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi nasara wajen shawo kan matsalar tsaro a ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata