DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 7, 2026
HomeBabban Labari Gwamnatin Nijeriya ta saki albashin watanni takwas na ma’aikatan jami’o’i

Gwamnatin Nijeriya ta saki albashin watanni takwas na ma’aikatan jami’o’i

Gwamnatin Nijeriya ta saki albashin watanni takwas da aka riƙe na mambobin kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya (SSANU), bayan ƙungiyar ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matakin gwamnatin ya zo ne ƙasa da sa’o’i 48 bayan SSANU ta bai wa gwamnatin wa’adin kwanaki 14 domin aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla ta 2026 da kuma biyan basussukan albashin da ma’aikatan ke bi.

Kungiyar ta bayyana buƙatunta ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taron majalisar zartarwartarta na kasa karo na 56, wanda aka gudanar a Jami’ar Uyo da ke jihar Akwa Ibom a ƙarshen makon da ya gabata.

SSANU ta yi gargaɗin cewa idan gwamnatin Nijeriya ba ta cika buƙatunta cikin kwanaki 14 ba, za ta koma yajin aikin sai baba ta gani, ba tare da sake bayar da wata sanarwa ba.

Kungiyar ta kuma buƙaci a biya mambobinta albashin watanni biyu da aka riƙe a lokacin yajin aikin ƙungiyoyin kwadago na shekarar 2022.

Haka kuma, SSANU na neman a biya ma’aikatan bashin shekara guda sakamakon ƙarin albashin kashi 25 cikin 100 da kuma kashi 35 cikin 100.

Sai dai ƙasa da sa’o’i 48 bayan bayyana wannan matsaya, gwamnatin Nijeriya ta saki kuɗin albashin watanni takwas, lamarin da ya taimaka wajen kauce wa yiwuwar sake samun tsaiko a ayyukan jami’o’in Nijeriya.

Shugaban SSANU na ƙasa, Comrade Mohammed Haruna Ibrahim, ya tabbatar da sakin kuɗaɗen, inda ya ce nan ba da daɗewa ba mambobin ƙungiyar za su fara samun saƙonnin shigar kuɗin albashinsu.

Ya bayyana matakin a matsayin abin da ke nuna cewa tattaunawa mai ma’ana tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ma’aikata, idan aka haɗa ta da ɗaukar mataki cikin gaggawa, na iya taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a wuraren aiki da kare haƙƙin ma’aikata.

SSANU ta yaba wa Ministan Ilimi, Farfesa Tunji Alausa, bisa rawar da ya taka wajen ganin an saki kuɗaɗen, tana mai cewa ya cika alƙawarin da ya yi na taimakawa wajen warware matsalar.

Shugaban ƙungiyar ya shawarci mambobin SSANU da ke rassan jami’o’i daban-daban da su tuntubi hukumomin jami’o’insu domin tabbatar da cewa an biya su kuɗaɗen da suka dace.

Ya kuma buƙaci ma’aikatan da su sanar da shugabancin ƙungiyar idan aka samu wani gibi ko aka kasa biyan su kuɗin da aka ware musu.

Kafin SSANU ta bayar da wa’adin, ministan Ilimi ya tuntubi shugaban ƙungiyar domin tabbatar masa da cewa ma’aikatar kuɗi da ofishin Akanta-Janar na Nijeriya suna aiwatar da matakan da suka dace domin sakin kuɗaɗen.

Sai dai duk da sakin albashin watanni takwas, SSANU ta jaddada cewa har yanzu gwamnati na da sauran basussuka da ya kamata ta biya, ciki har da albashin watanni biyu da aka riƙe a shekarar 2022 da kuma bashin shekara guda da ya samo asali daga ƙarin albashin kashi 25 da 35 cikin 100.

Kungiyar ta ce waɗannan kuɗaɗe haƙƙoƙin ma’aikata ne da ya kamata a biya ba tare da jinkiri ba.

SSANU ta kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da hukumomin gudanarwar jami’o’in jihohi da su tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar, tare da gargadin cewa nuna bambanci ko jinkirta biyan haƙƙoƙin ma’aikata na iya haifar da ƙarin rikici a tsarin jami’o’i.

Duk da haka, ƙungiyar ta ce tana nan daram kan matsayinta na neman warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da kuma tabbatar da zaman lafiya a wuraren aiki.

Ta kuma jaddada cewa za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da doka da kundin tsarin mulki suka tanada wajen kare haƙƙoƙin mambobinta idan aka kasa aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata